in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dan wasan tseren kasar Sin Liu Xiang ya halarci bikin bankawa da aka shirya masa
2015-05-21 10:35:11 cri


Shahararren dan wasan kasar Sin, wanda ya yi fice a gudu da tsallake shingaye Liu Xiang, ya cika da hawaye, lokacin da ya halarci gasar karshe da aka shirya domin yin bankwana da shi a birnin Shanghai.

Gasar wadda ta gudana a ranar Lahadi, ta samu halartar manyan 'yan wasan tsere, ciki hadda David Oliver, da Orlando Ortega, da kuma Aries Merritt. Liu ya kuma mika kofin gasar ta mita 110 da aka shirya domin shi ga wadanda suka yi nasara.

An dai nuna dinbin nasarorin da Liu ya samu ta babban allon dake filin wasan birnin na Shanghai, yayin da Liu ke share hawaye, kafin kuma ya gabatar da jawabin ban kwana. Ciki irin nasarorin da aka nuna hadda nasarar da ya samu a gasar Olympic ta kasar Switzerland, wadda ya halarta a shekarar 2006, da kuma janyewar da ya yi daga wasannin Olympic guda biyu a tarihin wasannin sa.

Manyan 'yan wasan 9 da suka yi fice a wannan fanni na tsere, sun kewaya filin wasan tare da Liu Xiang. Inda Liu ya rika daga hannu ga dubban al'ummar da suka halarci wannan biki. Daga karshe ya daga manyan yatsun sa biyu domin nuna matsayin kwarewar sa, kana ya rusunawa 'yan kallon a gabar da ake kammala bikin.

Liu dan shekaru 31 da haihuwa, ya bayyana shirin sa na yin ritaya ne daga harkar wasanni ne a ranar 7 ga watan Afirilu. Dama kuma masu nazarin wasanni sun yi hasashen hakan, tun bayan raunin da ya samu a farkon gasar Olympic ta shekarar 2012.

Liu wanda dan asalin birnin Shanghai ne, ya yi fice a gasanni daban daban da ya halarta, ciki hadda gasar Olympic ta 2004 inda ya lashe gudun mita 110, ya kuma karya matsayin bajimtar Jackson, bayan da ya kammala gudu cikin mintuna 12 da dakikoki 91.

Kaza lika ya kara karya matsayin bajimta a shekarar 2006, inda ya kammala tseren da ya shiga cikin mintuna 12 da dakikoki 88. Sai kuma gasar duniya ta birnin Osakan kasar Japan, inda Liu ya lashe ajin maza na gasar, da kuma gasar Olympic ta dauniya duka dai a wannan shekara.

Har wa yau Liu ya kammala tseren mita 110 a wasu karin wasannin, kafin raunin da ya hana shi shiga gasar Olympic ta birnin Beijing a shekarar 2008.

Bayan samun kulawar likitoci a lokuta daban daban, Liu ya fuskanci babbar matsalar kafa a gasar Olympic ta birnin Landan, ya kuma janye daga shiga wadda aka gudanar a Beijing. Lamarin da ya sanya wasu suka rika zargin hukumar wasannin motsa jiki ta kasar Sin, da laifin boye raunin da Liu ke fama da shi.

Za dai a dade ana tunawa da irin rawar da Liu ya taka a fannin wasannin motsa jiki, musamman ma a fagen tsere tare da tsallake shingaye inda ya yi fice. Kana wannan dan wasa ya shiga kundin tarihin kasar Sin, na 'yan wasa da suka yi fice, suka kuma shahara, tare da samun karbuwa tsakanin al'ummar Sinawa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China