in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ghana na shirin tunkarar gasar COSAFA
2015-05-07 10:37:28 cri
Kasar Ghana ta fara shirye-shiryen buga gasar kwallon kafa ta kasashen kudancin Afirka na bana, gasar da ake yiwa lakabi da COSAFA wadda kuma za ta gudana nan gaba cikin wannan wata na Mayu daga ranar 17 zuwa 30 ga watan.

Kaza lika kulaf din kasar Black Star zai buga gasar kwararrun kulaflikan nahiyar Afirka wato "Championship for African Nations", wanda hukumar CAF ke shiryawa, gasar da ita kuma za ta gudana a kasar Rwanda cikin shekarar mai zuwa.

Tuni dai kocin kungiyar ta Black Stars Maxwell Konadu, ya zabi 'yan wasa 26 domin fara atisaye a birnin Obuasi, tun daga ranar Litinin 4 ga wata, gabanin wasannin da za su buga a gasar ta COSAFA.

Ghana dai ta samu gurbin buga gasar ta kudancin Afirka ne, duk da kasancewar ta a yammacin Afirka, bayan da tsibiran Comoros ta janye daga halartar gasar. Kaza lika Ghanan za ta kasance kasa daya tilo daga yankin yammacin Afirka da za ta shiga wannan gasa, tun fara buga ta shekaru 17 da suka gabata. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China