150507-chelsea-ta-lashe-kambin-gasar-premier-league-bello.m4a
|
A wannan kaka, wani yanayin da ya sha bamban da na shekarun baya shi ne, Chelsea ta zama kan gaba tun farkon kakar wasan har zuwa karshe. Sa'an nan, kungiyar ta samu damar kiyaye wannan matsayi na ta, har zuwa wasan mako na 35, inda aka bayyana ta a matsayin wadda ta lashe gasar bisa tazarar maki da ta yiwa sauran kulaflikan dake buga gasar.
Bisa wannan nasara da Chelsea ta samu, babban kocin kungiyar Jose Mourinho, ya tabbatar da al'adarsa ta horas da kulaflika, wato sau da yawa kungiyar da yake jagoranta na fara cimma manyan nasarori a shekara ta 2 da fara jagorantar ta, duk da cewa a shekarar farko ba kasafai ake ganin tasirin aikin na sa sosai ba.
Idan za a iya tunawa yayin da ya fara jagorantar Real Madrid a shekarar 2010, ya bayyana cewa kungiyar da yake jagoranta ta kan samu babban ci gaba a shekara ta biyu, domin fasahar cocin ba za ta yi cikakken amfani ba sai zuwa shekaru 2 da fara aiwatar da ita. Kuma kungiyar ta Real Madrid ta cimma hakan, bayan da ta lashe kambin gasar La liga ta kakar wasan 2011-2012, ta yadda shi Mourinho ya cika alkawarin da ya dauka.
Bayan da Mourinho ya koma kungiyar Chelsea a shekarar 2013, akwai kungiyoyi 4 dake takara da juna a lokacin, wato su ne Arsenal, da Man. City, da Liverpool da kuma Chelsea. Ganin yanayin da ake ciki na fuskantar abokan karawa masu karfi, ya sa Mourinho ya yi hasashen cewa Chelsea ba za ta samu damar lashe kambin gasar Premier ta wannan shekara ba. Amma bayan da kungiyar ta shigo da Francesc Fàbregas, da Diego da Silva Costa a bara, Mourinho ya ce Chelsea ta shirye tsaf domin lashe kambin gasar. A yanzu haka muna iya cewa wancan hasashe na sa ya tabbata ke nan.
A wannan karo, wasan da ya tabbatar da lashe kofin na Premier shi ne wasan mako na 34, inda Chelsea ta kara da Arsenal, ta na mai neman kunnen doki kadai, kuma daga karshe sun tashi kunnen doki marasa ci. Sai dai wannan sakamako na rashin samun maki ko 1, ya sa wasu kafofin watsa labarun kasar Birtaniyan zargin Chelsea da kokarin kare kai, maimakon nuna cikakken karfin ta.
Amma duk da haka a hakika a wannan kakar wasa, Chelsea ta yi matukar kokarin taka rawar gani, musamman ma a farkon rabin kakar. Ga misali, a farkon wasanni 19 da kungiyar ta buga, Diego Costa ya halarci 15 daga cikinsu, inda ya ciwa kulaf din kwallaye 13. A iya cewa ke nan kwarewar da dan wasan ya nuna ta canza yanayin da Chelsea take ciki, ganin yadda a kakar wasa ta 2013 zuwa 2014, fitattun 'yan wasan kulaf din su 3 wato Fernando Jose Torres, da Samuel Eto'o, da Demba Ba, sun ci wa Chelsea kwallaye 15 ne kawai.
A na shi bangare, Francesc Fabregas, shi ma ya taka rawar gani a farkon rabin kakar wasan, inda ya tallafawa abokan taka-ledar sa cin kwallaye har karo 13 a wasanni 18 da ya buga. Haka kuma dan kasar Belgium Eden Hazard shi ma ya nuna kwarewarsa a farkon rabin kakar wasan, inda ya yi kokarin kutsa kai bangaren abokan karawarsu har karo 151, tare da samun nasarar cin kwallaye a karo 89.
Duk wadannan alkaluman nasara da fitattun 'yan wasan kungiyar Chelsea suka samu, suna kan gaba a tsarin gasar Premier ta Birtaniya a wannan kaka. Sai dai bayan da aka kusan kaiwa ga karshen wasanni na wannan kaka, al'adar Mourinho na rashin canza 'yan wasa ta sa kwararrun 'yan wasan kungiyar ta sa gajiya sosai. Musamman ma lokacin da wasan ya kai zagaye na 20, inda Tottenham Hotspur ta lashe Chelsea da ci 5 da 3. Daga wannan wasa, Chelsea ta canza salonta na buga kwallo, zuwa wani irin yanayi na taka-tsan-tsan, da neman hakikanin sakamako.
Kuma ko da bayan Diego Costa ya ji rauni, Chelsea ta ci gaba da samun nasarori karkashin wannan hali mai wuya. Ta haka kungiyar ta lashe abokan karawar ta a wasanni 11 da ta buga, gami da yin kunnen doki a sauran wasanni 4. Don haka ma iya cewa, kungiyar Chelsea ta yi kokarin buga wasanni masu dadin kallo a farkon rabin kakar wasan dake daf da kammala.
Kuma bayan da kungiyar ta fara fuskantar yanayin gajiyar 'yan wasan ta, da raunuka da wasun su suka samu, ta ci gaba da kokarin haye wahalhalu, tare da kare matsayinta a teburin gasar ta Premier. Wadannan bangarori 2 sun tabbatar da matsayin kungiyar na jagorar gasar Premier.
Hakika dai Mourinho ya riga ya canza yanayin kungiyar Chelsea sosai, ganin yadda ya sayar da wasu 'yan wasa masu tsada, tare da shigo da wasu nagartattun 'yan wasa da ba su da tsada sosai. Wannan mataki na da ma'ana, ganin yadda ake kalli Chelsea, a matsayin kulob mai bada fifiko kan amfani da fitattun 'yan wasa, gami da kallon shi Mourinho a matsyin wani coci mai son kashe kudi a baya. Amma a kakar wasa ta 2014 zuwa 2015, Chelsea ta sayar da 'yan wasa 8 da suka hada da David Luiz, da Demba Ba, da Romelu Lukaku, da André Schürrle. Sa'an nan ta yi amfani da kudin da ta samu, ta sayo wasu 'yan wasa 6, da suka kunshi Francesc Fabregas, da Diego Costa, da dai sauransu. Ta wannan mataki kulaf din ya samu damar daidaita tsarin sa, tare da tsimin kudi har fam miliyan 1.4.
Ban da haka kuma, idan mun dubi tarihin kungiyar Chelsea, za mu ga cewa, kambin da ta samu a wannan karo yana da ma'anar musamman, ganin ya kasance karo na 4 da kungiyar ta lashe kambin gasar Premier, lamarin da ya sanya kungiyar zama ta biyu, wajen yawan lashe kambin. Sa'an nan shi kansa Mourinho, za a iya kwatanta nasarorin da ya samu, da na kwararrun masu horar da 'yan wasan kuloflikan gasar Premier, kamarsu Arsène Wenger, da Alex Ferguson, kuma yana da damar wuce saura wajen yawan samun nasarori, ganin yanzu shekarunsa 52 ne kawai, wato bai kai tsufan da zai yi ritaya ba tukuna.(Bello Wang)