Ujah dan shekaru 24, wanda kuma dan asalin Najeriya ne, ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru hudu ga sabon kulaf din na sa, bayan da ya kammala gwajin lafiya a 'yan kwanakin baya. Saboda haka Cologne zai rasa babban dan wasan sa sakamakon wannan sauyi, dan wasan da ya ci kwallaye 10 a kakar wasannin da ke daf da kammala.
Da yake tsokaci game da sayen Ujah, babban daraktan kulaf din Bremen Thomas Eichin, ya ce sun dade suna lura da takun dan wasan, sun kuma tabbatar dan wasa ne dake da sauri, da kuzari, wanda kuma zai taka muhimmiyar rawa a kulaf din na su.
Shi dai Ujah ya fara takawa Cologne kwallon ne tun cikin shekarar 2012, inda bisa jimilla ya taimaka wajen cin kwallaye 10, ya kuma ci kwallaye 34 cikin wasannin 104 da ya buga, tun daga shekarar 2012 kawo wannan lokaci.
A gida Najeriya, Ujah ya bugawa Super Eagles wasa na farko tsakanin ta da Mexico cikin watan Yunin shekarar 2013. Ya zuwa yanzu kuma ya bugawa kulaf din kasar ta sa manyan wasanni 5.
Cologne dai na matsayin na 11 a gasar BundesLiga ta Jamus, yayin da Bremen dake matsayi na 7, ke fafutukar samun gurbin buga gasar zakarun turai a kakar badi. (Saminu Alhassan)