A cewar shugaban hukumar ta NBBF Tijani Umar, kulaflikan kwallon Kwando na maza da na mata, za su fara atisaye a birnin Abuja fadar mulkin kasar, inda ake sa ran 'yan wasan kasar dake gida da na waje, zasu hallara domin gwada kwarewar su, gabanin fidda wadanda za su wakilci kasar a gasannin biyu.
Cikin tsare-tsaren da mahukuntan NBBF suka bayyana, hadda gudanar da wasannin share fage na sada zumunta, tsakanin Najeriya da wasu kulaflikan dake nahiyar Turai da kuma kasar Sin. Kana za su gudanar da ran-gadin samun horo a Amurka, kafin ranar 30 ga watan Mayun da muke ciki, lokacin da kulaf din mata na kasar zai fara buga wasannin a gasar Afrobasket, a birnin Abidjan, fadar mulkin kasar Cote D'Ivoire.
Za kuma a gudanar da gasar All-Africa Games karo na 11 a birnin Brazzaville na kasar Congo, tsakanin ranekun 4 zuwa 19 ga watan Satumbar bana.(Saminu Alhassan)