in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Atletico Madrid ta tsawaita kwantiragin Saul Niguez
2015-05-07 10:39:34 cri
Kulaf din Atletico Madrid ya tsawaita kwantiragin dan wasan kasar Sifaniya Saul Niguez da shekaru 5. Shi dai wannan dan wasa na taka leda ne a ajin matasa 'yan kasa da shekaru 21, inda a yanzu zai bugawa Atletico Madrid din wasa har ya zuwa shekarar 2020.

Hakan dai na nuna cewa Saul Niguez zai samu damar taka leda sosai a shekaru 5 masu zuwa, a daya daga manyan kulaflikan Sifaniya a matsayin shahararren dan wasa matashi. A kakar wasan data gabata dai an bada Saul bashi ga Rayo Vallecano inda ya taka leda a matsayin dan wasan baya.

Sai dai bayan komawar sa Atletico Madrid, ya koma buga kwallo a tsakiyar fili, inda ya buga wasanni 32 a kakar bana, ya kuma ci kwallaye 4.

A cewar mahukuntan kulaf din na sa, Saul ya samu cikakken horo tun daga mataki na kasa, ya kuma kai ga matsayi na dan wasan dake buga ajin kwararru na kulaf din cikin kyakkyawan yanayi da bajimta.

Yanzu haka dai Saul na ci gaba da kasancewa daya daga 'yan wasan Sifaniya ajin 'yan kasa da shekaru 21, inda yake rike da mukamin kyaftin din tawagar.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China