in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rikicin Sudan ta Kudu ya tsananta hadarin jin kai
2015-05-18 15:14:36 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya ba da sanarwa ga manema labaru a jiya Lahadi, inda ya yi Allah wadai da munanan rikice-rikicen da suka faru a jihohin Unity da Upper Nile na kasar Sudan ta kudu, kuma ya mai da hankali sosai kan matsalar jin kai da ya kara tsananta a kasar.

Sanarwar ta ce, bangarori biyu da suka yi musanyar wuta a kasar Sudan ta Kudu sun haddasa tada tarzoma a tsakaninsu, lamarin da ya sa mutane fiye da dubu 100 suka rasa gidajensu, kana mutane fiye da dubu 300 ba su iya samun tallafin jin kai ba. Kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da yadda bangarorin biyu suka ki martaba yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka cimma, inda ya jaddada cewa, ba za a iya kawo karshen rikicin kasar ba ta hanyar daukar matakan soja.

Ban da haka kuma, kwamitin sulhu na MDD ya bukaci bangarori daban daban na kasar da su shiga kokarin da ake na shimfida zaman lafiya da neman bakin zaren daidaita batun ta hanyar siyasa. A sa'i daya kuma, kwamitin sulhun ya nemi bangarorin daban daban na kasar da su dakatar da kawo cikas kan aikin sojojin wanzar da zaman lafiya na MDD da masu ba da agaji da ke kasar.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China