in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kimanin 'yan gudun hijira 4500 na sansanin MDD dake Sudan ta Kudu
2015-04-08 11:05:56 cri

Kimanin mutane 4500 ne suka yi hijira a baya bayan nan zuwa wani sansanin MDD na Malakal dake jihar Upper Nile na kasar Sudan ta Kudu, in ji kakakin MDD Stephane Dujarric a ranar Talata.

Lamarin da ya kai ga adadin fararen hula a wannan wuri zuwa kusan mutane dubu 26, kuma gaba daya fiye da dubu 115 a dukkan fadin kasar da suka yi gudun hijira a sansanonin MDD, in ji mista Dujarric a yayin wani taron manema labarai. Wannan shi ne adadi mafi girma na 'yan gudun hijira da tawagar MDD ke karewa tun farkon barkewar wannan rikici a cikin watan Disamban shekarar 2013.

Haka kuma akwai wasu sabbin 'yan gudun hijira da sauran abokan huldarmu da suka rawaito a sauran yankunan kasar Sudan ta Kudu, har ma aka hada da 'yan gudun hijira dubu 31 dake jihar Jonglei, in ji kakakin MDD.

Kasar Sudan ta Kudu ta fada cikin rikici a cikin watan Disamban shekarar 2013, inda aka samu fito na fito tsakanin sojojin dake biyayya ga shugaba Salva Kiir da masu goyon bayan tsohon mataimakin shugaban kasar Riek Machar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China