in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yaba amincewa da Sudan ta Kudu ta yi kan yarjejeniyar kare 'yancin yara
2015-05-05 09:39:32 cri

Kwamitin kare hakkin yara na MDD ya yaba matakin da kasar Sudan ta Kudu ta dauka na amincewa da yarjejeniyar da aka cimma game da 'yancin kare hakkin yara, inda ya nanata kiran da yake kan a amince da yarjejeniyar a duniya baki daya.

Bugu da kari kwamitin ya bukaci kasashen da har yanzu ba su amince da yarjejeniyar ba, ciki har da kasar Amurka da su hanzarta yin hakan ba tare da bata lokaci ba.

Don haka, kwamitin ke bukatar kasashen da suka sanya hannu kan wannan doka, ciki har da kasar Sudan ta Kudu a yanzu haka, da su sauki nauyin da ke kansu na martaba tare da kare 'yancin yara, wanda ya hada da 'yancin yin rayuwa, samun kiwon lafiya, ilimi da yin walwala.

Sauran sun hada da 'yancin iyali da 'yancin kare su daga tashin hankali da rashin nuna musu wariya ko bambanci da kuma 'yancinsu na fadin ra'ayi.

Yanzu kasar Sudan ta Kudu ce kasa ta 195 a duniya da ta amince da wannan doka, da aka aiwatar a shekarar 1989. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China