Game da batun warware matsalar kasar Sudan ta Kudu, babban abin da ke kan gaba shi ne a ba da goyon baya ta hanyar da ta kamata domin a tattauna tsakanin bangarorin biyu dake gaba da juna domin su cimma matsaya daya nan ba da dadewa, da kuma aiwatar da yarjejeniyar da aka amince a kai.
Liu Jieyi, babban wakilin kasar Sin a MDD wanda ya rike shugabancin kwamitin sulhu na watan Fabrairu ya sanar da hakan lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a karshen wa'adin shugabancin shi a ranar Jumma'an nan.
Mr. Liu ya ce, ko kwamitin sulhun majalissar, ko kuma sauran kasashen duniya, kowane ya kamata ya bi tunanin abin da zai fi dacewa da kasar ta Sudan ta Kudu, sannan ya ba da gudummuwa yadda ya kamata tun da yanzu haka bangarorin biyu da ke gaba da juna suna tattaunawa.
A mika takaradar share fage ga kwamitin sulhun a farkon wannan makon wanda ya bayyana takunkumin a kan duk mutumin da zai nemi kawo tsaiko a batun tattaunawar zaman lafiya a kasar.
Shirin sulhunta bangarorin biyu da ake na baya bayan nan a karkashin sa idon kungiyar raya gwamnatocin gabashin Afrika IGAD, an fara shi ne a birnin Adis Ababa na kasar Habasha a ranar Litinin din da ya gabata. (Fatimah)