Sakatare janar na MDD, Ban Ki-moon ya sanar a ranar Laraba da nada Moustapha Soumare na kasar Mali a matsayin mataimakin manzon musamman na tawagar MDD dake kasar Sudan ta Kudu.
A cewar wata sanarwa da aka fitar ta ofishin kakakinsa, mista Soumare zai maye gurbin Raisedon Zenenga na kasar Zimbabwe, da shi kuma za'a nada shi mataimakin manzon musammun na tawagar MDD dake kasar Somaliya. Ta bakin kakakinsa, mista Ban ya nuna godiyarsa ga mista Zenenga kan aikinsa da taimakon da ya bayar ga ayyukan MDD a kasar Sudan ta Kudu.
Bisa babbar kwarewarsa kan harkokin zaman lafiya, da ci gaban al'umma da na siyasa, mista Soumare shi ne a yanzu haka mataimakin manzon musamman na tawagar tabbatar da zaman lafiya ta MDD a kasar DRC-Congo, inda kuma shi ne jami'in kula da harkokin jin kai, kana wakilin hukumar tsare-tsare da raya kasa ta MDD wato UNDP a wannan kasa, mukamin da yake rike da shi tun a cikin watan Oktoban shekarar 2012. (Maman Ada)