Kakakin ma'aikatar harkokin cinikayya ta kasar Sin Shen Danyang ne ya bayyana hakan a gun taron manema labaru da aka gudanar a kwanakin baya inda ya bayyana alamun musamman na hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka. Na farko shi ne kayayyakin injiniyoyi sun sa kaimi ga fitar da kayyayakin zuwa kasashen Afirka cikin sauri. Yawan kayayyakin da Sin ta fitar zuwa nahiyar Afirka a watanni 4 na farkon wannan shekara ya karu da kashi 21.8 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Na biyu shi ne yawan sabbin yarjejeniyoyin gina kayayyakin more rayuwa da bangarorin biyu suka daddale ya karu sosai. Yawan kudin da yarjejeniyoyin suka shafa a watanni 3 na farko na bana ya kai dala biliyan 23.11, wanda ya karu da kashi 49.4 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara. Hakazalika kuma,ana fuskantar koma baya wajen zuba jari a bangaren manyan ayyukan more rayuwa a hadin gwiwar, da raguwar saurin fitar da kayayyaki daga Sin zuwa Afirka sakamakon raguwar farashin manyan kayayyaki da dai sauransu.
Shen Danyang ya kara da cewa, za a gudanar da taron ministoci karo na 6 na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka a bana, yana fatan za a yi amfani da wannan dama, da shiga ayyukan gina manyan tsari uku a Afirka da fara hadin gwiwar samar da kayayyaki a tsakanin Sin da Afirka, ta haka za a gaggauta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya mai inganci da bunkasuwa a tsakaninsu. (Zainab)