Kakakin ma'aikatar Shen Danyang ne ya bayyana hakan a Jumma'ar nan, yana mai cewa cikin kasashe 10 dake kan gaba a yawan yarjejeniyoyin da suka daddale tare da kasar ta Sin, 7 kasashe ne na nahiyar Afirka, kuma ana samun babban ci gaba a fannin zuba jari a manyan ayyuka a nahiyar.
Shen Danyang ya kara da cewa, yanzu haka ana fuskantar matsin lamba a bangaren raguwar bunkasar tattalin arzikin nahiyar Afirka, don haka kasar Sin ke fatan za a yi amfani da damar taron ministoci karo na 6, na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka da za a gudanar a bana, don gaggauta sa kaimi ga hadin gwiwar tattalin arziki, da cinikayya a tsakanin sassan, da kuma kyautata tsarin da ake da shi a wannan fanni. (Zainab)