Shen Danyang ya bayyana haka ne a yayin taron maneman labaran da aka saba yi na ma'aikatar kusuwancin a wannan rana. Ya kuma bayyana cewa, fannonin da kasar Sin za ta horas da 'yan kasashe masu tasowa na Asiya da Afirka za su hada da harkokin siyasa, noma, tattalin arziki, gina kayayyakin more rayuwa da kuma kiyaye muhalli da dai sauransu. Kana kasar Sin za ta ba da horo ta hanyar kafa azuzuwan nazari na gajeran lokaci da kuma azuzuwan ba da horaswa a nan kasar Sin, haka kuma, za ta ba da takardun shaidar samun wadannan horo, da kuma shirya azuzuwan ba da horaswa a ketare, domin yin musayar fasahohin neman ci gaba tare da kasashe masu tasowa na Afirka da Asiya, da kuma yin musayar fasahohi tsakanin kasashen, ta yadda za a iya ciyar da bunkasuwar kasashe masu tasowa na Asiya da Afirka gaba. (Maryam)