Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ta yi bayani kan huldar diflomasiyyar Sin da Afirka
A kwanan baya, akwai rahotanni da ke cewa, sabo da kasar Sin na bukatar samun albarkatun kasa da sauran makamashin halittu daga kasashen Afirka, ta yadda za ta iya biyan bukatunta na samun ci gaba, ana ganin cewa, shi ya sa kasar Sin take yin gine-ginen kayayyakin more rayuwar jama'a a wasu kasashen Afirka domin ta fake kan dogara da siminti wajen bunkasa huldar diflomasiyya a tsakaninta da kasashen Afirka. Game da irin wannan magana, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yau Laraba 28 ga wata cewa, abubuwan da Sin ke gudanarwa a Afirka ya nuna cika alkawarinta na taimaka wa kasashen Afirka wajen samun dauwamammen ci gaba.
Hua Chunying ta jaddada cewa, "ya kamata a shimfida hanyoyin mota da farko idan ana son samun wadata", wannan wata muhimmiyar fasaha ce da kasar Sin ta samu cikin shekaru sama da 30 da suka gabata yayin da take samun bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri bayan da ta aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje.
Hua ta kara da cewa, kasar Sin ta dade tana taimaka wa kasashen Afirka wajen samar da kayayyakin more rayuwa, domin taimakawa kasashen Afirka samun kyautatuwar zaman rayuwar al'umma. Haka kuma, kasar Sin na son ci gaba da yin hadin gwiwa da wasu kasashe domin taimaka wa kasashen Afirka wajen samun dauwamammen ci gaba. (Maryam)