Kasri wanda ya bayyana hakan a taron dake gudana a birnin Jakarta dake kasar Indonesia ya kuma kara da cewa, yanzu haka kasashen Afirka suna samun bunkasuwa cikin sauri, kana suna kokarin koyi daga fasahohin kasashen Asiya. A daya hannun kuma kasar Sin da kasashen Afirka, suna kiyaye kyakkyawar dangantaka, yayin da Sin ke taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa hadin gwiwar dake tsakanin Asiya da Afirka.
Daga nan sai ya bayyana kyakkyawar alakar dake tsakanin kasarsa da kasar Sin, kasashen da ya ce suna sada zumunta tsawon lokaci. Kaza lika ya bayyana aniyar kasar Tunisia, ta kara inganta kawancen dake tsakaninta da kasar Sin, tare da gudanar da shawarwari a tsakanin sassan biyu, musamman game da batun hadin gwiwa tsakanin Afirka da kasar ta Sin. (Zainab)