in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Ireland
2015-05-18 10:26:37 cri

A yammacin jiya Lahadi ne, firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Ireland Enda Kenny a birnin Shannon. Inda Mr. Li Keqiang ya nuna farin ciki game da ganawarsu a yayin da ya yada zango a kasar Ireland.

Mr. Li ya kara da cewa, kasar Sin da kasar Ireland sun dade suna fahimtar juna da nuna goyon baya ga juna kana akwai dankon zumunci tsakanin jama'ar kasashen biyu. Ban da haka kuma, Mr. Li ya gabatar da sakamakon da kasar Sin ta samu wajen raya tattalin arziki, kuma yana fatan bangarorin biyu za su yi amfani da kwarewarsu a fannin tattalin arziki domin kara yin ciniki da musayar al'adu.

Kazalika, Mr. Li Keqiang ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatan kungiyar EU za ta zama wata hadaddiyar kungiya mai wadata, Sin tana son samun sakamako mai kyau wajen yin hadin gwiwa tare da kungiyar domin inganta huldar bangarorin biyu har ma da tattalin arzikin duniya.

A nasa jawabin Mr. Enda Kenny ya nuna maraba ga Li Keqiang. Ya nuna cewa, kasar Ireland na dora muhimmanci sosai kan makomar tattalin arzikin kasar Sin, kuma ya jinjinawa matakan gyare-gyare da gwamnatin kasar Sin ta dauka kan tattalin arzikinta.

Bugu da kari tana dora muhimmanci sosai kan huldar da ke tsakaninta da kasar Sin, tana kuma fatan shugabannin kasashen biyu za su rika tuntubar juna da kara yin musayar ra'ayi a fannonin cinikayya da aikin gona da hada-hadar kudi da hayar jiragen sama da bunkasa makamashi maras gurbata muhalli da harhada magunguna da tarbiyya da yawon shakatawa da sauransu. Kasar Ireland tana son taimakawa kamfanonin kasar Sin wajen zuba jari a kasashen Turai.

Bayan shawarwarin, firaministocin biyu sun kuma gana da manema labaru tare.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China