in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da shugaban bankin duniya
2013-09-17 20:46:22 cri

A ranar Litinin din nan 16 ga wata firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugaban bankin duniya Jim Yong Kim tare da alkawarin karfafa dangantaka da bankin, wanda ke da cibiya a birnin Washington na kasar Amurka.

A lokacin ganawar, Mr. Li ya yaba ma hadin gwiwar da yanzu haka yake a tsakanin kasar Sin da bankin duniya, yana mai cewa, hanyar ciyar da inganta tattalin arzikin duniya ita ce mai da hankali kan batun ci-gaba.Ya yi bayanin cewa, kasar Sin tana farin cikin ganin bankin yana aiwatar da shirinsa yadda ya kamata wajen taimaka ma kasashe masu tasowa tare da rage radadin talauci, don haka a shirye take na aiki tare da bankin don magance matsalolin da suka shafi ci-gaban duniya baki daya tare da wani yunkurin da zai kawo inganci a tattalin arzikin duniya.

Firaministan har ila yau ya yi bayani ma shugaban bankin duniyan game da kwaskwarimar da kasar ke yi da kuma ci-gaban da ta samu, yana mai jaddada amfanin kirkire-kirkire ba lallai ta hanyar fasaha ba kadai har ma ta hanyar dabaru, manufofi da yadda za a aiwatar da su.

A nasa bangaren shugban bankin duniyan Jim Yong Kim ya ce, bankin duniya yana yaba yadda gwamnatin Sin ta kudiri matsin lamba na ganin ta yi kwaskwarima sannan bankin ta yaba kwarai a game da hanyoyin da kasar ke bi wajen aiwatar da shirinta, don haka in ji shi bankin ke son kara hadin gwiwa da Sin don inganta shirye-shiryenta a tattalin arziki.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China