in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na mai da hankali ga tabbatar da tsaftacacciyar gwamnati
2014-02-12 11:06:06 cri

Mahukunta a kasar Sin, sun sha alwashin tabbatar da wanzuwar budaddiyar gwamnati mai cike da tsafta.

Firimiyan kasar ta Sin Li Keqiang ne ya bayyana hakan, yayin da yake jawabi gaban wakilan majalissar kasar, a taronta da ya jagoranta ranar Talata 11 ga watan nan.

Li ya ce, za a tabbatar da daukar dukkanin matakan da suka wajaba, domin kakkabe ayyukan cin hanci da rashawa, da ma dukkanin wasu huldodi da suka sabawa doka daga sassan aikin hukuma. Don haka ne ma firimiyan kasar ta Sin, ya bukaci daukacin jagororin dake rike da madafan iko, da su tabbatar da bin managarcin tsarin gudanar da ayyukan hukuma.

Har ila yau ya yi kira ga hukumomin binciken yadda ake kashe kudaden hukuma, da su kara gwazo wajen tattara managartan bayanai, tare da bankado asirin dukkanin wani tsari da ya sabawa dokar kasa. Ya ce, an samu babban ci gaba a yakin da ake yi da cin hanci da rashawa a shekarar da ta gabata, sai dai har yanzu akwai sauran rina a kaba.

Daga nan sai ya alkawarta aiwatar da manyan manufofin tsaftace ayyukan hukama guda 8, da gwamnatin tarayyar kasar ta amince da su a shekarar 2012. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China