in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Li Keqiang ya gana da wakiliyar shugaban kasar Amurka
2015-04-14 16:20:30 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da wakiliyar shugaban kasar Amurka kuma ministar kasuwancin kasar Penny Pritzker, da kuma tawaga mai kula da harkokin cinikayya ta shugaban kasar dake karkashin jagorancinta.

A lokacin ganawar tasu Mr. Li Keqiang ya bayyana cewa, huldar kasashen Sin da Amurka na kara taka rawa a duniya, don haka Kasar Sin tana son samun karin imani da juna, da karfafa hadin gwiwa, da daidaita sabanin ra'ayin da ake samu tsakaninta da kasar Amurka yadda ya kamata, domin tinkarar kalubaloli daban daban da aka samu a wasu yankuna gami da duk duniya baki daya tare, ta yadda za a kara ciyar da huldar dake tsakaninsu gaba.

A cewar firaministan kasar Sin, huldar cinikayya ta zama tushe ne ga huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka. Haka kuma kasashen biyu ke iya taimakawa juna a fannin tattalin arziki, tare da samun makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa a fannonin gina kayayyakin more rayuwar jama'a, da makamashi, da aikin sadarwa, da kuma kiyaye muhalli.

A bangaren nata, Penny Pritzker ta ce, wannan karo ne na farko da kasar Amurka ta tura wata tawagar cinikayya dake karkashin kulawar shugaban kasar Amurka zuwa kasar Sin, don haka aikin yana da ma'ana sosai a fannin tarihi, haka kuma ya shaida cewa, kasar Amurka ta dora muhimmanci sosai kan huldar cinikayya a tsakaninta da kasar Sin, tana fatan bangarorin biyu za su kara yin cudanya a fannin kasuwanci. Ta jaddada cewa kasar Amurka tana son kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannonin samar da tsabtaccen makamashi da yin tsimin makamashi da kuma sauran wasu fannoni daban daban, kuma tana fatan kasashen biyu za su yi hadin gwiwa wajen habaka kasuwa a kasashen waje, kuma ta nuna maraba da karin kamfanonin kasar Sin da su zuba jari a kasar Amurka. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China