Firayim minstan kasar Sin Li Keqiang ne ya bayyana wannan buri na kasar ta Sin a jiya ranar Jumma'a 1 ga watan nan na Nuwamba a yayin bikin bude taron masu ruwa da tsaki kan bunkasa ci-gaban duniya, da samar da jagoranci na gari da aka fara a nan birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin.
Li ya ce, a wannan lokaci da Sin ke kokarin warware matsalolin tattalin arziki da na zamantakewar al'umma, a hannu guda mahukuntan na sa kaimi ga samar da sauye-sauye masu ma'ana, tare da bude kofofin yin hadin gwiwa da ragowar kasahen duniya. Hakan a cewarsa, zai haifar da kyakkyawan yanayin bunkasuwa, da cimma moriyar juna a matakan shiyya-shiyya da na kasa da kasa.
Firayim minstan kasar ta Sin ya kara da cewa, wajibi ne a dauki managartan matakan samar da daidaito, da bunkasa zaman lafiya a cikin gida, muddin ana fatan samarwa al'ummar kasar sama da miliyan dubu guda kyakkyawar rayuwa a zamanance. (Saminu)