A yayin ganawar, mista Li ya nuna cewa, har kullum kyautata hadin gwiwar abokantaka a tsakanin Sin da kasashen Afirka, muhimmiyar manufa ce ga kasar Sin. A cikin sabon halin da ake ciki, kasar Sin na son hada kai da kasashen Afirka wajen yin amfani da kyakkyawar dama da daidaita kalubaloli tare, a kokarin samar da yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali wajen tabbatar da samun bunkasuwa, da kuma kara raya huldar abokantaka irin na sabon salo a tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare.
A nasa bangaren kuma, mista Pinda ya ce, Tanzaniya tana gode wa kasar Sin bisa goyon bayanta kan harkokin bunkasuwar Afirka cikin lumana. Don haka kasarsa na son inganta hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Sin bisa tsarin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, a kokarin taka rawa wajen bunkasa dangantaka a tsakanin Afirka da Sin. (Tasallah)