in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar dakaru ta Houthi ta kasar Yemen ta amince da farfado da shawarwarin siyasa
2015-05-15 15:11:30 cri

Wani jami'in gwamnatin kasar Yemen ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kungiyar dakaru ta Houthi ta kasar ta amince da farfado da yin shawarwarin siyasa tare da sauran kungiyoyin kasar bisa sharadin dakatar da farmakin sama da kasar Saudiyya da sauran kasashe ke yi, domin kawo karshen rikicin kasar.

Wani jami'in ma'aikatar watsa labaru da ya boye sunan sa ya ce, bayan da aka yi shawarwari tare da manzon musamman mai kula da harkokin Yemen na MDD, wakilan kungiyar Houthi da tsohon shugaban kasar Ali Abdullah Saleh sun amince da farfado da shawarwarin siyasa da MDD ke shugabanta bisa sharadin dakatar da farmakin sama da kasar Saudiyya da sauran kasashe ke kai wa kasar Yemen, amma sun nemi yin shawarwarin a birnin Geneva, ba a Riyadh ba, babban birnin kasar Saudiyya, wanda kasashen yankin Gulf suka nemi yin shawarwari a ciki.

Ban da haka kuma, kakakin MDD Stephane Dujarric ya bayyana a jiya Alhamis cewa, babban magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya bayyana a yayin da ya buga waya ga mataimakin shugaban kasar Yemen Khaled Bahah cewa, za a yi shawarwari a tsakanin bangarori daban daban na kasar Yemen a wata kasa ta daban.

Ban da haka kuma, Ban Ki-Moon ya ce, dole ne a tsagaita bude wuta cikin gejeren lokaci domin aikin jin kai.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China