A daren jiya Lahadi, jiragen saman yaki na kasar Saudiyya da sauran kasashen da abin ya shafa sun ci gaba da kai farmaki ta sama kan dakarun Houthi dake kasar Yemen. Mahukuntan kasar Yemen sun ce, farmakin da aka fara tun daga safiyar ranar Alhamis din makon jiya ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar mutuwa da raunatan mutane fiye da 100.
Wani jami'in sojojin gwamnati da ba ya so a bayyana sunan shi ya ce, jiragen saman yaki na kasashen Saudiyya da sauransu sun kai farmaki ga sansanonin dakarun Houthi dake birnin Sanaa, babban birnin kasar Yemen da jihar Ta'izz dake kudancin kasar a daren ranar lahadi.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Yemen ta bayar da sanarwa a jiya cewa, mutane 13 sun mutu a yayin farmakin da aka kai a ranar 28 ga wata da dare. A wannan rana kuwa, ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta ba da labarin cewa, ya zuwa daren ranar Asabar, mutane 35 sun mutu a sakamakon farmakin, a yayin da mutane 88 suka ji rauni.
Hanyoyin filin jiragen sama na kasa da kasa dake birnin Sanaa sun lalace a yayin farmaki, amma jami'in filin ya sanar da cewa, an kammala aikin gyara hanyoyin saukar jiragen sama na fararen hula a ranar asabar din.(Lami)