in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon: Shawarwari ne hanya daya tilo ta kawo karshen rikicin Yemen
2015-03-27 15:38:23 cri

Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, ya yi kira ga bangarori daban daban da rikicin kasar Yemen ya shafa, da su tabbatar da tsaron fararen hula, da ma'aikatan dake gudanar da aikin jin kai. Mr. Ban wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa ta hannun kakakinsa a jiya Alhamis, inda ya jaddada cewa komawa teburin shawarwari ne hanya daya tilo da ta dace a bi, domin kawo karshen rikicin kasar Yemen.

Sanarwar ta ce, Ban Ki-Moon ya lura da cewa, kasar Saudiyya ta dauki matakan soja a kasar Yemen ne domin biyan bukatun gwamnatin kasar, wanda kuma ya samu amincewa daga wasu mambobin kungiyar hadin gwiwar kasashen Larabawa dake yankin Gulf wato GCC. Ban Ki-Moon ya ce zai ci gaba da sa ido kwarai kan halin da ake ciki a kasar ta Yemen.

Ban da haka kuma, sanarwar ta ce, kwamitin sulhu na MDD ya bayar da sanarwar shugaba a ranar Lahadin da ta gabata, don goyo bayan shugaban kasar Yemen Abdu Rabbih Mansour Hady.

Daga nan sai Ban Ki-Moon ya yi kira ga bangarori daban daban da wannan lamari ya shafa, da su kaucewa daukar matakai da ka iya haifar da cikas ga manufar dinkewar kasar Yemen, da 'yancin kanta, da kuma cikakken yankunan kasar. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China