Dangane da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying ta bayyana a yayin taron manema labarai da aka saba yi a yau cewa, kasar Sin na fatan bangarorin da abin ya shafa za su aiwatar da sabuwar yarjejeniyar Minsk yadda ya kamata, domin ci gaba da warware matsalar kasar Ukraine ta hanyar siyasa, da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar Ukraine, har ma a duk fadin Turai cikin sauri. Sa'an nan kuma, kasar Sin na fatan gamayyar kasa da kasa su ci gaba da ba da gudummawa kan wannan batu. (Maryam)