A daya hannun kuma, ministocin harkokin wajen kasashen Faransa, da Jamus, da Rasha da Ukraine, sun yi kira da a aiwatar da yarjejeniyar Minsk yadda ya kamata.
Bisa labarin da kafofin watsa labarun kasar Ukraine suka fitar, an ce wani babban jami'in sojin jamhuriyyar Donetsk Eduard Basurin, ya bayyana cewa dakarun sa kai sun shirya janye manyan bindigogin harba bama-bamai har 96 daga yankin da ake gumurzu a ranar 24 ga wata.
Kaza lika shi ma kakakin "jamhuriyyar Luhansk" ya bayyana cewa, Luhansk ta fara gudanar da aikin janye manyan makamai tun daga ranar 17 ga watan nan. Ya ce batun ko za a gaggauta kammala wannan aikin ko a'a, ya dogara ga yadda hukumomin kasar Ukraine suka dauki nasu matakai.
A nasa bangare kakakin rungumar yaki da ta'addanci ta kasar Ukraine, ya ce dakarun dake gabashin kasar Ukraine ba su janye manyan makamai daga yankin da ake fafatawa ba, maimakon hakan, suna shirin sake jibge wadansu makaman ne ma. Ya ce sharadin farko na janye manyan makamai shi ne aiwatar da matakin farko na yarjejeniyar Minsk, wato ta tsagaita bude wuta. Kuma tun da ya zuwa yanzu ba a kai ga tsagaita bude wuta ba, mahukuntan kasar Ukraine ba za su tattauna kan shirin janye na su manyan makaman ba.
A wani ci gaban kuma ministocin harkokin wajen kasashen Faransa, da Jamus, da Rasha da Ukraine, sun tattauna a birnin Paris, bayan zantawar tasu ne kuma suka fidda wata sanarwa, suna masu kira ga bangarori 2 da rikicin Ukraine ya shafa, da su aiwatar da yarjejeniyar Minsk, wadda ta tanaji tsagaita bude wuta, da janye manyan makamai, karkashin sa idon kungiyar tsaro da hadin gwiwar Turai. (Zainab)