in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin kare hakkin bil Adama na MDD ya amince da rahoton da Sin ta gabatar kan hare 'yancin dan Adam a kasar
2013-10-28 20:34:07 cri
Rahoton da MDD ta fitar game da kare hakkin bil Adama a kasar Sin ya yi kyau matuka, in ji kakakin ma'aikatar harkokin kasashen wajen kasar Sin Hua Chunying.

Da take bayani ga manema labarai a ranar Litinin din nan 28 ga wata, Madam Hua ta ce, rahoton game da kasar Sin ta gabatar kan kare hakkin dan Adam a kasar ya samu amincewar jami'an dake aikin a cikin kwamitin kare hakkin bil Adama na majalisar a ranar Jumma'ar da ta gabata .

Muhimmin abin da ke cikin rahoton yana da sakamako mai kyau. Kuma rahoton ya yi nazarin ayyukan kare hakkin bil Adama na kasar Sin cikin adalci kuma yadda ya kamata.

Sakamakon wannan rahoto, wakilai daga kasashe daban daban sun mika fatansu na alheri ga kasar Sin, in ji Madam Hua.(Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China