Yayin rufe taron na wannan karo mataimakin shugaban kungiyar manazarta hakkin dan Adam ta kasar Sin Ye Xiaowen, ya bayyana cewa dandalin tattaunawar ya mai da hankali kan sha'anin bunkasa harkar kare hakkin dan Adam na kasar Sin, kana mahalarta dandalin tattaunawar sun bayar da ra'ayoyinsu kan ma'anar kare hakkin dan Adam, da batun mu'amala tsakanin kasa da kasa a wannan fanni.
Sauran batutuwan da aka tattauna sun hada da kirkiro hanyoyin aiwatar da harkokin kasa, da tabbatar da hakkin dan Adam, da daidaita tsakanin ayyukan yaki da ta'addanci da kare hakkin dan Adam.
Kaza lika an samu kyakkyawan sakamako a zaman dandalin tattaunawar, matakin da zai taimaka wajen bunkasa sha'anin kare hakkin dan Adam na kasar Sin da ma a sauran sassan duniya baki daya.
Ban da wannan kuma, Ye Xiaowen ya kara da cewa, kasar Sin na fatan amfani da dandalin tattaunawar wajen yin mu'amala tare da sauran kasashe a wannan fanni, da sa kaimi ga sha'anin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa. (Zainab)