in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bangarori daban daban na kasar Sin sun shiga aikin bada ceto a kasar Nepal
2015-05-08 16:12:41 cri

Kwanaki fiye da 10 bayan abkuwar girgizar kasar da ta afkawa kasar Nepal, har yanzu ana ci gaba da gudanar da aikin bada ceto a kasar. Ya zuwa yanzu, Sin ta samar da gudummawar jin kai da darajarsu ta kai kudin Sin Yuan miliyan 60 ga kasar Nepal. Mataimakin ministan harkokin ciniki na kasar Sin Qian Keming ya yi bayani cewa, Sin tana daya daga cikin kasashen da suka fi saurin samar da gudummawa ga kasar Nepal bayan faruwar girgizar kasar, kuma a nan gaba Sin za ta tsara sabon shirin bada taimako bisa halin da ake ciki a kasar.

A jiya Alhamis 7 ga wata ne, ma'aikatu 7 na kasar Sin kamar ma'aikatar harkokin jama'a, da ta harkokin waje, da harkokin ciniki, da hukumar kiwon lafiya da kayyade iyali da sauransu suka gudanar da taron manema labaru a ofishin watsa labaru na kasar, inda aka yi bayani kan halin da ake ciki game da aikin bada ceto a kasar Nepal da yankin Tibet na kasar Sin. Mai bada taimako ga ministan harkokin ciniki na kasar Sin Liu Jianchao ya yi bayani cewa, bayan girgizar kasa ta faru a kasar Nepal, Sin tana daya daga cikin kasashen da suka fi saurin samar da gudummawa ga kasar. Ya ce,

"Bayan abkuwar girgizar kasar da dare, nan da nan rukunin bada ceto da hukumar kula da harkokin girgizar kasa ta kasar Sin ta tura ya tashi zuwa kasar Nepal, wanda ya zama babban rukunin bada ceto na farko da ya isa birnin Katmandu. Kana tawagar farko ta likitoci da gwamnatin kasar Sin ta tura da rukunin bada ceto da rukunin likitocin da bangaren soja na kasar Sin ya tura sun isa kasar Nepal a ranar 27 da kuma ranar 28 ga watan Afrilu, don neman mutanen da suka bace da bada jinya ga mutanen da suka ji rauni a sakamakon girgizar kasa ba tare da bata lokaci ba."

Game da halayen musamman da rukunin bada ceto na kasar Sin ya fuskanta yayin da yake aiki a kasar Nepal, mataimakin ministan harkokin ciniki na kasar Sin Qian Keming ya bayyana cewa,

"Na farko, Sin ta kasance kasar da ta fi saurin bada gudummawa ga kasar Nepal bayar faruwar girgizar kasar. Na biyu, ban da rukunonin bada ceto da samar da kayayyakin gudummawa cikin gaggawa da gwamnatin kasar Sin ta tura, kuma tawagogin bada ceto na al'umma da masu aikin sa kai da kamfanonin Sin da Sinawa dake kasar Nepal su ma sun shiga aikin bada ceto nan da nan."

An ce, gwamnatin kasar Sin ta sanar da samar da gudummawar jin kai zagaye biyu ga kasar Nepal. Ya zuwa yanzu, Sin ta samar da kayayyakin da suka kai nauyin ton 546 da darajarsu ta kai kudin Sin Yuan miliyan 60 ga kasar Nepal, ciki har da tantuna dubu 8 ga yankin da ke fama da bala'in yake bukata. Kasar Nepal ta karbi kashin farko na kayayyakin gudummawa da Sin ta samar, inda ta rarraba su ga jama'ar kasar, yayin da kashi na biyu na gudummawar ke kan hanyar zuwa kasar Nepal.

Sin ta bada gudummawa a yayin da kasar Nepal take fuskantar bala'i mai tsanani, gwamnatin kasar Nepal da jama'ar kasar har ma wakilin MDD da sauran rukunonin bada ceto na kasashen duniya sun nuna yabo ga kasar Sin. Mataimakin ministan harkokin ciniki na kasar Sin Qian Keming ya bayyana cewa, Sin za ta tsara sabon shirin bada gudummawa bisa la'akari da halin bala'in da ake ciki a kasar Nepal. Ya ce,

"Ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin da ofishin jakadancin Sin dake kasar Nepal suna yin mu'amala, da tsara sabon shirin samar da gudummawa bisa la'akari da halin bala'i da aikin bada ceto da ake ciki a kasar Nepal. Za kuma a tura rukunin binciken game da aikin sake gina kasar bayan bala'in, da samar da gudummawa ga kasar Nepal a fannonin zaman rayuwar jama'a da ayyukan more rayuwa don taimakawa jama'ar kasar Nepal yadda za su sake gina gidajensu." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China