Da yammacin yau Alhamis din nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tashi daga birnin Beijing zuwa birnin Astana, fadar mulkin kasar Kazakhstan.
Kasar ta Kazakhstan dai za ta zamo ta farko cikin kasashen 3 na Asiya da Turai, da shugaba Xi zai kai ziyarar aiki a wannan karo cikin kwanaki 6, bisa gayyatar da shugaban kasar Nursultan Abishevich Nazarbayev, da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin, da kuma shugaban kasar Belarus Alexander Gligolievich Lukasenko suka yi masa.
Bisa tsarin ziyarar dai shugaba Xi zai fara isa kasar Kazakhstan, kafin ya tashi zuwa kasar Rasha, domin halartar bikin tunawa da ranar cika shekaru 70 da cimma nasarar yakin kiyaye kasar Rasha, sa'an nan ya kammala da ziyarar aiki a kasar Belarus. (Lami)