141218-an-gudanar-da-cikakken-zaman-taro-na-127-na-kwamitin-harkokin-wasannin-olympics-na-duniya-zainab.m4a
|
Cikin jawabin sa sarki Albert II ya nuna farin matuka bisa zabar Monaco domin gudanar da cikakken zaman taron 127 na kwamitin IOC. A matsayin shugaban sashen kula da wasanni, da kiyaye muhalli na kwamitin IOC, Albert II ya jaddada cewa, kasar Monaco na dora muhimmanci kwarai kan harkokin wasannin motsa jiki hadi da na kiyaye muhalli.
Shi kuwa a nasa jawabi a gun bikin kaddamar da cikakken zaman taron, shugaban kwamitin IOC Thomas Bach jinjinawa kasar Monaco ya yi, bisa kokarin ta na gudanar da wannan taro. Bach ya yi nuni da cewa, ana bukatar kyautata tsarin wasannin Olympics, domin cimma nasarorin gudanar da wasannin, bisa gudummawar da wasannin ke baiwa rayuwar jama'a. don haka ya ce ya zama wajibi a tsaya tsayin daka wajen inganta gasar ta Olympics.
A ranar 8 ga watan nan ne dai aka gabatar da shawawari game da aiwatar da kwaskwarima 40, a ajandar wasannin Olympics ta shekarar 2020, a gun cikakken zaman taron, kana aka jefa kuri'u kan shawarwarin. A karshe kuma dukkan masu jefa kuri'un suka amince da shawarwarin 40.
Bayan taron na wannan rana, Bach ya bayyanawa taron manema labaru cewa, bai taba tunanin shawarwarin 40 da ya gabatar, za su samu amincewa daga dukkan mambobin kwamitin na IOC ba.
A ganinsa, wannan ya bayyana cewa, dukkan mambobin kwamitin IOC na kokarin gudanar da kwaskwarima, da kyautata tsarin wasannin Olympics. Ana dai daukar shirin na kwaskwarima da Bach ya gabatar, a matsayin shirin inganta makomar wasannin Olympics a shekaru 15 masu zuwa na kwamitin IOC.
Cikin matakan na kwaskwarima 40, abu mafi jawo hankali shi ne, gyara aikin neman samun iznin daukar bakuncin gudanar da gasar wasannin Olympics, da wasannin da ake yi a yayin gasar, da rage kudin da ake kashewa wajen gudanar da gasar, da kuma neman bunkasuwa mai dorewa a wasannin na Olympics.
Ban da wannan kuma, a ranar 9 ga wata da safe, yayin cikakken zaman taron 127 na kwamitin IOC, an jefa kuri'u, tare da tsaida kudurin shigar da kwamitin harkokin wasannin Olympics na kasar Kosovo a cikin kwamitin IOC, da sanya kasar cikin mambobin kwamitin su 205.
Shugaban kwamitin harkokin wasannin Olympics na kasar Kosovo Vittorio Cassani, ya nuna godiya ga kwamitin IOC, domin amincewa da ta yi da kwamitinsa. Ya bayyana cewa, kwamitinsa zai ci gaba da yin kokari, da bin ka'idojin Olympics, da kuma aiwatar da shirin yin kwaskwarima na ajandar wasannin Olympics ta shekarar 2020, wanda aka zartas a gun cikakken zaman taron na wannan karo.
Kungiyar kasar Kosovo za ta halarci gasar wasannin motsa jiki ta nahiyar Turai karo na farko, da za a gudanar a kasar Azerbaijan a watan Yuni na shekarar badi. (Zainab)