in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasafin kudin wasannin Olympics na Rio de Janeiro ya kai dala biliyan 16.3
2014-08-15 09:29:12 cri
Magajin birnin Rio de Janeiro Eduardo Paes, ya ce kasafin kudin wasannin Olympics na birnin Rio de Janeiro na shekarar 2016 dake tafe, ya kai dala biliyan 16.3.

Mr. Paes wanda ya bayyana hakan ga taron manema labaru don gane da wasannin Olympics din da birnin na Rio de Janeiro ke shirin karbar bakunci, ya kuma ce akwai ayyuka da dama da suka hada da gine-gine, da na ayyukan more rayuwa da za a gudanar a filayen wasa, koda yake ya yi imanin birnin zai iya kammala dukkanin wadannan ayyuka, ya kuma gudanar da wasannin yadda ya kamata.

Mr Paes ya bayyana cewa, an kasa kasafin kudin wasannin na Olympics kashi uku. Na farko akwai kudin da kwamitin wasannin na birnin Rio de Janeiro zai yi amfani da su, wajen gudanar da wasannin nakasassu, wato dala biliyan 3.

Sai kashi na biyu wanda gwamnatin kasar za ta zuba domin samar da ababen more rayuwa na bukatar wasannin Olympics din, wato dala biliyan 2.8.

Kashi na uku kuwa ya kunshi kudin da gwamnatin kasar za ta kasha, wajen kyautata sufuri da muhalli a kasar, wato dala biliyan 10.5.

Bisa jimilla dai za a kashe dala biliyan 16.3, wanda kuma kashi 57 cikin dari na yawan su zai fito ne daga hukumomi masu zaman kansu, ya yin da ragowar kashi 43 cikin dari na kudin, zai fito daga dukiyar kasa.

Ban da wannan kuma, Mr Paes ya ce, koda yake cimma nasarar gudanar da gasar kofin duniya ta kasar Brazil, ta kawar da damuwar kasashen duniya game da dar-dar da ake yi da kasar ta Brazil wajen shirya wasanni, amma duk da hakan birnin Rio de Janeiro, zai ci gaba da shiri domin samun nasarar gudanar da wasannin na Olympics yadda ya kamata, domin tabbatar nasarar wasanni a shekarar 2016 cikin nasara. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ga Wasu
v Tarihin wasannin Olympics 2013-08-01 20:18:10
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China