Ana fatan dai masu aikin sa kan da yawan su ya kai mutum dubu 70, za su bada hidima ya yin wasannin Olympics da za a gudanar a karo na farko a nahiyar kudancin Amurka.
Akwai dai nau'oin ayyuka iri-iri da yawan su ya kai fiye da 500, wadanda masu aikin sa kan za su gudanar ya yin wasannin na Olympics na birnin Rio de Janeiro. Irin wadan nan ayyuka sun hada da aikin tafinta, da tukin ababen hawa, da bada taimako, da aikin jarida, da na likitoci da dai sauransu.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, tun daga ranar 28 ga wata, za a kasa daukar irin wadannan ma'aikata zuwa matakai uku. Inda za a fara da yin rajistar a shafukan internet, sa'an nan kwamitin wasannin Olympics zai gudanar da jarrabawa ga wadanda suka yi rajista a fannin harsuna da dai sauransu. Sai mataki na biyu, wanda ya kunshi shirya kwas na harsunan waje, da abinci, da tufaffin musamman na wasannin Olympics, da dai sauransu. Kana bayan kammala wasannin na Olympics, masu aikin sa kan za su samu takardun halartar wasannin. (Zainab)