Mr. Yu ya fadi haka ne lokacin da yake jawabi a bikin kaddamar da taron dandalin tattaunawa tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan karo na 6 da aka fara yau a birnin Xiamen na lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin.
Sannan Mr. Yu ya kara da cewa, yayin da ake kara bunkasa dangantakar dake tsakanin bangarori biyu na mashigin tekun Taiwan, tabbas za a gamu da wasu matsaloli masu tsanani. Sai dai abu mafi muhimmanci da ya kamata a yi shi ne gudanar da kome bisa matsayin 'yan uwantakar bangarorin biyu dake matsayin iyali daya, ya ce, ya kamata a kara fahimtar juna, a girmama juna da kuma hakuri da juna. Lokacin da ake kokarin daidaita sabani da matsalolin da ke wanzuwa tsakanin bangarorin biyu, lallai akwai bukatar yin kokari tare wajen magance su baki daya. (Sanusi Chen)