in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar 'yan sanda ta Philippines ta amince da harben wani mai kamun kifi na yankin Taiwan na kasar Sin har mutuwa
2013-05-10 17:04:36 cri
A ranar 10 ga wata da safe, jagoran hukumar yankin Taiwan na kasar Sin Ma Ying-jeou ya bayyana cewa, hukumar yankin za ta yi binciken lamarin harben wani mai kamun kifi na gundumar Pingdong har mutuwa da jirgin ruwan Philippines ya yi, yana mai bukatar gwamnatin Philippines da ta nemi gafara game da batun a hukunce, da gurfanar da masu laifin gaban kuliya, sannan ta biya kudin diyya ga iyalan mamacin. A ranar 10 ga wata da tsakar rana ne dai, hukumar 'yan sanda ta teku ta Philippines ta ba da sanarwa, inda ta amince da cewa, 'yan sanda masu sintirin teku na kasar sun harbe wani jirgin ruwan kamun kifaye na yankin Taiwan na kasar Sin.

A wannan rana da safe, wani jami'i mai kula da harkokin waje na yankin Taiwan Shi Ding ya zanta da wakilin kasar Philippines dake yankin Taiwan Bai Xili. Bayan zantawarsu, Bai Xili ya ce, wannan lamari wani abun bakin ciki ne, kuma ya nemi gafara da nuna ta'aziyarsa ga iyalan mai kamun kifaye da ya mutu. Ya ce, hukumar shari'a ta Philippines za ta gudanar da bincike cikin hadin gwiwa tare da takwaranta ta yankin Taiwan, don tabbatar da hujjar harbin bindigarta da wurin da abin ya faru, kuma idan aka gano cewa, hakan ya saba ma doka, to Philippines za ta dauki matakai yadda ya kamata.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China