in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin tana adawa da Amurka kan yadda ta sayar da makamai ga yankin Taiwan
2014-04-09 16:23:52 cri

A 'yan kwanakin baya, majalisar wakilai ta kasar Amurka ta zartas da kudurin 'amince da muhimmimancin dokar hulda da Taiwan, da sayar da jiragen ruwan yaki ga yankin'. Game da haka, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin Mista Geng Yansheng ya bayyana a ran 9 ga wata cewa, yayin da ake ganawa da ministan tsaron kasar Amurka Charles Hagel, kasar Sin ta riga ta bayyana matsayinta kan matakin Amurka, wato kasar Sin a tsayawa take tsayin daka wajen adawa da Amurka kan yadda ta sayar da makamai masu zamani ga Taiwan. A cewar kakakin, kasar Sin tana rike da wannan matsayi ne a fili, kuma ta dade tana tsayawa a kansa.

Geng ya sake nanata cewa, batun Taiwan yana da nasaba da mulkin kai da cikakken yankin kasar Sin, wanda ya shafi babbar moriyar kasar. Don haka Sin ta bukaci Amurka da ta girmama babbar moriyar Sin da abubuwan da take lura da su, don ta dauki matakan da za su ciyar da dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu da sojojin kasashen biyu gaba. (Danladi)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China