Game da hakan, Brigedia janar Geng Yansheng, kakakin ma'aikatar tsaron kasar Sin ya sanar da cewa, bangaren Sin ya yi matukar hassala da wannan shiri, wato bangaren Sin yana nan a kan matsayinsa na kin amincewa da kasar Amurka ta sayar wa yankin Taiwan makamai, da matsayinsa na tsaron iyakokinsa, da kwanciyar hankali da cikakken yankin kasar.
Brigedia janar Geng Yansheng ya nuna cewa, da kakkausar harshe bangaren Sin ya nemi kasar Amurka da ta mutunta ainihin moriyar kasar Sin da muhimman abubuwan da take kulawa. Ya kuma nemi kasar Amurka da ta daina sayar wa yankin Taiwan makamai da yin mu'amala ta fuskar aikin soja tsakanin Amurka da yankin Taiwan na kasar Sin, kuma ta daina lalata dangantakar soja dake tsakanin kasashen biyu na Sin da Amurka da rundunoninsu.
Brigedia janar Geng Yansheng ya kara da cewa, bangaren Sin zai kara mai da hankali kan batun, kuma zai dauki matakin mayar da martani a duk halin da ake ciki. (Sanusi Chen)