Wani babban jami'i na hukumar yankin Taiwan na kasar Sin Jiang Yihua, ya kira wani taron manema labaru a ranar 15 ga wata, inda ya sanar da sanya ma kasar Philippine karin takunkumi, wanda ya kunshi matakai 8 da aka dauka.
Matakan takunkumi nan 8 su ne, takaita yawon shakatawa a kasar Philippine, dakatar da mu'amala tsakanin manyan jami'an bangarorin 2, daina ayyukan hadin gwiwa a fannonin cinikayya, tattalin arziki, ayyukan gona, da kamun kifi, gami da dakatar da hadin kai da bangarorin 2 suke yi a fannin kimiyya da fasaha.
Ban da haka, hukumar Taiwan ta riga ta tura jiragen ruwan yaki da dama, don gudanar da atisayen soja a yankin teku dake kudu da tsibirin Taiwan, tare da jiragen ruwan 'yan sandan tsaron bakin teku.
A nata bangaren, fadar shugaban kasar Philippine ta sanar a ranar 15 ga wata da cewa, shugaban kasar Benigno Aquino ya riga ya tura manzonsa zuwa yankin Taiwan a wannan rana, don rokon gafara kan yadda sojojin kasar suka harbe wani dan yankin Taiwan mai sana'ar kamun kifi ba bisa wata hujja ba, haka zalika ya yi alkawarin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamari.(Bello Wang)