Da wani ci gaban kuma, mataimakin shugaban jam'iyyar ta NCP Ibrahim Ahmed Ghandour, ya ce jam'iyyar tasu ta riga ta cimma matsaya daya da jam'iyyar adawa ta Umma, wadda ta amince ta goyawa shirin kafa sabuwar gwamnati baya.
Bugu da kari, Ghandour ya yi Allah wadai da tashe-tashen hankulan da dakarun SPLA suka haddasa a yayin babban zaben kasar, inda ya ce ba za a gudanar da shawarwari da kungiyar ba, har sai ta canja akidunta. (Maryam)