Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Son Hong Lei wanda ya bayyana hakan a yau yayin taron manema labarai, ya kuma bayyana kudurin kasar Sin na bunkasa sabon ci gaba a hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Sudan.
Ya ce, kasancewar Sin muhimmiyar abokiyar Sudan, kasar ta Sin na mutunta zabin al'ummar Sudan kuma a shirye Sin take ta taimakawa kokarin Sudan na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al'ummar kasar.
A jiya ne hukumar zaben kasar Sudan ta ayyana Al-Bashir a matsayin mutumin da ya lashe zaben shugaban kasar bayan da ya samu kashi 94.5 cikin 100 na kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar. (Ibrahim)