Jam'iyyun siyasar kasar 45 da suka hada da kananan jam'iyyu da dama ne dai suka shiga zaben na wannan karo.
Rahotanni sun bayyana 'yan takarar shugabancin kasar ta Sudan 16 ne za su fafata a zaben, ciki hadda da shugaba mai ci Omar Al-Bashir, ko da yake wasu daga jam'iyyun adawar kasar sun kautacewa shiga zaben.
Al'ummar kasar kimanin miliyan 13 da dubu dari 6 ne ake zaton za su kada kuri'unsu a zaben, a rumfunan zaben da yawansu ya kai 7000.
Bisa tsarin zaben dai za a fafata neman kujerun 'yan majalissar dokokin kasar 1,072, da kuma kujerun 'yan majalissar jihohi 2,235. Za kuma a ci gaba da kada kuri'u ya zuwa ranar Laraba, kafin kuma a fara kidayar kuri'u a ranar Alhamis. Kazalika ana fatan bayyana sakamakon zaben a ranar Litinin 27 ga watan nan.
Kungiyoyi da hukumomin kasa da kasa da dama ne dai ke sanya ido game da zaben, wadanda suka hada da wakilan IGAD, da na AU, da kuma na kungiyar kasashen Larabawa. (Saminu Alhassan)