Shugaban hukumar zaben kasar (NEC) Mukhtar al-Asam wanda ya bayyana hakan yau yayin taron manema labarai ya ce, shugaba al-Bashir ya samu kuri'u 5,252,478 cikin kuri'u 6,091,412 da aka kada, yayin da Fadi Elsid Shuaib ya zo na biyu da kashi 1.43 cikin 100 na kuri'un da aka kada.
A zaben na wannan karo shugaba al-Bashir ya fafata da 'yan takara 15 ne inda wasu daga cikin suka wakilci kananan jam'iyyu, yayin da wasu kuma suka tsaya a matsayin indifenda.
Sai dai ba kamar zaben shekarar 2010 ba, a wannan zaben manyan jam'iyyun adawa sun kaucewa zaben. (Ibrahim)