Bayan da aka samu goron gayyata daga gwamnatin Sudan, shugabar kwamitin kungiyar AU Nkosazana Dlamini Zuma ta amince da tura kungiya mai sa ido ta AU mai suna AUEOM zuwa kasar Sudan don babban zaben kasar da na majalissun kasar.
A ranar 10 ga wata, AU ta aika masu sa ido 20, wadanda suka fito daga kasashen Afrika 14 zuwa kasar Sudan don sa ido kan babban zaben kasar cikin wani gajeren lokaci, kuma wadannan mutane 20 sun wakilci kungiyar majalisar dokoki ta Pan-Afrika wato PAP, da hukumar kula da zaben ta EMBs da kungiyar kula da zamantakewar al'umma da jama'a ta CSOs.
Kungiyar AUEOM dake karkashin shugabancin tsohon shugaban kasar Nijeriya Olusegun Obasanjo ta isa birnin Khartoum a jiya, kuma za ta tuntubi masu zabe don sa ido game da ayyukan jefa kuri'a da kuma kidayar kuri'u.(Bako)