in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sudan ya yi kashedin shiga Sudan ta Kudu domin kai farmaki kan dakaru masu adawa da gwamnati
2015-04-30 20:42:15 cri

A yau kamfanin dillancin labaru na kasar Sudan ya ruwaito shugaba Omer Hassan Ahmed Elbashir na kasar na bayani a kwanakin baya cewa, idan kungiyar da ke adawa da gwamantin Sudan wato JEM, wadda ke samun goyon bayan gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta sake kai hari a yankin Darfur ta Kudu, to, Sudan za ta shiga Sudan ta Kudu domin mayar da martani kan kungiyar.

Shugaba Elbashir ya fadi haka ne a yayin da yake yiwa rundunar sojan kasar jawabi a yankin kudancin Darfur. A cewarsa, gwamnatinsa ta bukaci Sudan ta Kudu da ta kwance damarar kungiyar JEM. Idan ba a ba haka ba to, Sudan za ta dauki matakin da take ganin shi ya fi dacewa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China