in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gudanar da babban zaben Sudan yadda ya kamata, in ji tawagar sa ido ta Sin
2015-04-16 20:05:24 cri
Tawagar sa ido kan babban zaben shugabancin kasar Sudan daga kasar Sin, ta kira taron manema labarai a Alhamis din nan, inda ta yaba da yadda babban zaben kasar Sudan ke gudana.

Tawagar ta ce harkokin gudanar babban zaben sun dace da ka'idojin adalci, da kare 'yancin kai, ba kuma tare da boye komai ba. Shugaban tawagar Zhang Xun ya bayyana cewa, tawagar wadda ke karkashin jagorancinsa, ta ziyarci wasu tashoshin kada kuri'u, domin ganin yadda tsarin kada kuri'un ke gudana, inda ta tabbatar da cewa jama'ar kasar suna kada kuri'u cikin kyakkyawan yanayi.

Ya kuma kara da cewa, bisa binciken da tawagar sa idon ta gudanar, kasar Sudan ta shirya babban zaben a fannoni daban daban kuma yadda ya kamata, inda a dukkanin tashoshin kada kuri'u, aka samar da wakilan jam'iyyu, da wasu wakilan kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda ke sa ido ga yanayin zaben.

Bugu da kari, Mr. Zhang ya ce kasar Sin na fatan babban zaben shugabancin kasar Sudan na wannan karo zai taimakawa kasar, wajen ciyar da yunkurin siyasarta gaba, da ma ciyar da yanayin zaman lafiyar yankin gaba. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China