Kudurin wanda ya tanaji tsawaita wa'adin aikin tawagar da watanni 6, ya kuma bukaci dakarun bangarorin biyu da su dakatar da kaiwa ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD hare-hare. Yanzu haka dai sabon wa'adin aikin tawagar zai kammala ne a ranar 30 ga watan Yunin badi.
An kuma jaddada cewa, Syria da Isra'ila suna da alhakin aiwatar da yarjejeniyar shiga tsakanin sojojin sansan na su wadda aka cimma a shekarar 1974 a dukkan fannoni, kana bai kamata a gudanar da duk wani nau'i na aikin soja a yankin da aka killace ba.
Kaza lika kudurin ya kalubalanci kasashe membobin MDD, da su yiwa dakaru masu adawa na kasar Syria matsin lamba, game da yankin da tawagar masu sa idon ta MDD ke aiki a ciki, har wa yau an bukace su da su dakatar da daukar duk wani mataki daka iya kawo illa ga tsaron ma'aikatan kiyaye zaman lafiya na MDD. (Zainab)