Shugaban kasar Ghana John Mahama ya kira ga gamayyar masu hannu da shuni da su soke basussukan kasashen yammacin Afrika uku dake fama da cutar Ebola, da suka hada da Guinee, Laberiya da Saliyo.
Mista Mahama dake kuma shugabancin kungiyar tattalin arzikin yammacin Afrika (ECOWAS), yayi wannan kira a albarkacin ziyarar ministan huldar tattalin arziki na kasar Jamus, Gerd Muller, da kuma ministan kiwon lafiyar kasar Jamus Hermann Groehe suka kai a kasar Ghana. A cewarsa, Cutar Ebola ta kassara tattalin arzikin kasashen Laberiya, Saliyo da Guinee sosai.
Cutar Ebola ta haddasa illoli masu tsanani ga wadannan kasashe uku ta fuskar tattalin arziki, kuma kamar yadda bankin duniya ya ce, annobar ta janyo raguwar GDP da kashi 4.6 cikin 100, in ji mista Mahama. Ya bayyana cewa soke basussukan zai taimakawa wadannan kasashe daidaita tattalin arzikinsu da daukar wani sabon yunkurin cigaba.
Wadannan kasashe uku da suka fi fama da cutar Ebola suna bukatar goyon bayan gamayyar kasa da kasa, domin kara kokarinsu ta yadda zasu fuskanci irin wadannan matsalolin a gaba da kuma kyautata tsarin kiwon lafiyar jama'ar kasashensu.
Mista Mahama, yayi wannan kira da sunan kungiyar ECOWAS a yayin taron baya bayan nan na kungiyar tarayyar Afrika (AU) a birnin Addis Abeba. (Maman Ada)