Bisa wani sabon rahoto game da cutar Ebola da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fitar, an ce, a makon da ya gabata ne, aka tabbatar da cewa an samu mutane 30 da suka kamu da cutar Ebola a kasashen Guinea, Liberiya, da Saliyo da ke yankin yammacin kasashen Afrika, kuma yawan karuwar mutanen da suka kamu da cutar shi ne mafi kankanta tun daga watan Mayun shekarar bara.
Rahoton ya ce, tun daga ranar 30 ga watan Maris zuwa ranar 5 ga watan Afrilu, yawan mutanen da suka kamu da cutar ya ragu zuwa 21 a kasar Guinea, a yayin da wannan adadi ya kai 57 cikin makon da ya gabata. A kasar Saliyo ma, wannan adadi ya kai 9, kuma ya ragu har ma kwanni 5 a jere, yayin da kasar Liberiya ma, ba a samu wadanda suka kamu da cutar ba, kuma a dukkan fadin kasar, ba a samu sabbin mutane masu kamu da cutar ba cikin makwanni 6 da suka gabata.
Bisa sabuwar kididdigar da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta fidda, an ce, ya zuwa ranar 5 ga watan Afrilu, an gano mutanen da aka tabbabar ko zaton kamuwa da cutar Ebola da yawansu ya kai 25515 a kasashen Guinea, Liberia, da Saliyo, kuma cutar ta haddasa mutuwar mutane 10572.(Bako)