Kudurin ya nuna goyon baya ga kasar Yemen da ta dunke barakar kasar da samun ikon mallaka da cikakken yankin kasar, kana ya yi kira ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su cimma daidaito kan tsagaita bude wuta cikin hanzari, tare da bukatar bangarorin kasar da su warware matsala ta hanyar yin shawarwari cikin lumana.
Zaunannen wakilin Sin dake MDD Liu Jieyi ya yi jawabi bayan da aka zartas da kudurin cewa, kuduri mai lamba 2216 da kwamitin sulhun ya zartas yana da muhimmanci sosai wajen maido da zaman lafiya a kasar Yemen da kuma warware matsalar kasar ta hanyar siyasa. Karfin soja ba zai warware matsalar daga tushe ba, yayin da yin shawarwarin siyasa ita shi ne hanya daya tilo da za a bi wajen warware martsalar. (Zainab)